Wednesday, 20 July 2016

KOYI ZANA YANAR GIZO A SAUƘAƘE
Shin mi ake kira da yanar gizo?
Yanar gizo tana nufin wata irin ragace wadda ta haɗe da juna wajen samar da alaƙa a tsakanin su.To haka yanar ke tana nufin hanyar sadarwatar kwamfuta mafi sauƙi.Komi ya sata ta zama mafi sauƙi? Ba komai yasa ta zama mafi sauƙi ba sai dan haɗa alaka da tayi da duk wani nau’in abin sadarwa indai yana amfanbi da wutar lantarki ,da kuma haske.
 Yana gizo wurine da aka tanada dan samar da bayanai kowaɗanne iri kuma a cikin kowane irin yare a duk duniya gabaɗaya.sannan ita kanta yanar ana gina tane ta hanyar wasu ƙa’idoji,ba tare da su ba kuwa yanar zata kasance marar ma’ana, ƙa’idojin kuwa sun haɗa ne da yaruka iri daban-daban,sai dai a cikin yarukan akwai manya guda ukku,wanda in ba tare da su ba,yanar ba zata yiwuba.yaru kan sune:
1-HTML,tana nufin yaren da zai daidaita ita yanar ta zo a yarda aka buƙace ta. A sani ba abune mai sauƙi ba,a ce an zana yanar gizo da hannu ko fensiriba.saboda yarda yanar ke tafe da zane-zane kala-kala,saboda haka dole ne a samu wata hanya da zata bada damar zana shi a duk yarda mutum ya so,saboda haka aka ƙirƙiro html.Ita dai kalmar H-tana nufin HYPER,T-kuma tana nufin TEXT,M kuma tana nufin MARK-UP,L kuma tana nufin LANGUAGE,saboda haka duka kalmomin na nufin Hypertext mark-up language.Kuma dole kowa ne irin shafi zaka zana,sai kayi amfani da wannan ƙa’ida,sannan a sani wannan ƙa’ida ana kiranta da html tag.Tag wasu alamomi ne da suka haɗa <!#@({[“ da dai sauransu,wanda dole ne amfani da su.
2-CSS,yare na biyu kuwa shine CSS.Css dai na nufin CASCADING STYLE SHEET,wannan yare ko mi yasa ya zama na biyu kuwa? A sani yana gizo kowa yana son ya zana,amma dai kuma kowa yana da yarda yake son ta kasance,misali: wani yana son ace tana ɗauke da hotuna,wata kuma zane ne ake son a yi na wasu abubuw3a,ko furanni,da dai sauran su.To a ƙa’ida ya kamata a ce akwai kala,da zata inganta ita kanta yanar gizon ;don ba tare dsa kala ba yanar gizon bata kasance mai armashi da sha’awaba,saboda haka sai aka ƙirƙiro kala,kuma kalar yare na biyu da za’a buƙata a wurin zana yanar gizo.
3-JAVASCRIPT,haƙiƙa mtane da dama sun san javascript amma ta baka,kuma java yayi suna fiya da kowane yaren kwamfuta,ko saboda me? Ba saboda komai ba kuwa sai don kawai saboda yaren da yake da sauƙin sarrafawa,kuma sai ya kasance ma,babu kwamfutar da bata fahimtar sa,saboda damarmaki da ya bayar wajen sarrafa kwamfuta,misali:browser tana jin yaren java,kuma tana fahintar sa.zai wuya a samu kwamfutar da bata jin yaren
ABUBUWAN DA AKE YI DA YAREN
Mafi yawanci,GAME da ake yi na kwamfuta da shi ake yi,sannan ana amfani da shi wajen ƙirƙirar ƙwayar cutar kwamfuta da dai sauran su,wanda sannu a hankali za a koye su a wannan shafi.
 Zauna a gaban kwamfutar ka,ka buɗe ta,idan ta buɗe sai ka latsa inda aka rubuta START dan ka fara zana shafin ka na farko da kanka.Na tsu da kyau dan ka samu halin zama gwani kamar sauran,kana iya fina ni da ke koya ma wannan aiki.
!
Hoto 1.0 latsa START da ɓeran kwamfutar ka,watau (mause)
Bayan ka latsa shi zai nuna maka rubutu wanda hakan ke nuni da furogiram ɗin da ke cikin kwanfutar,{a sani wannan koyarwa ce da akayi komai cikin sauƙi,kuma a window,saboda haka kar ka jaraba a LINUX ko UNIX idan kana buƙata a tuntuɓe ni}bayann nan sai ka latsa PROGRAMME,idan ka latsa programme zai nuna maka wannan hotan na ƙasa.
Hoto 1.01,bayan ka latsa PROGRAMME jika a ACCESSORIES ka latsa.
Idan ka latsa accessories,zai nuna maka wani rubutun furogiram kamar haka:
Hoto 1.03,lissafa da inda aka rubuta Accessiblity har zuwa takwas.
Idan ka zo in da aka rubuta NOTPAD .
Hoto 1.04,inda aka rubuta notepad latsa wurin.idan ka latsa wurin zai ɓuɗe ma allon rubutu kamar haka:
Hoto 1.05,yanzu kau kayi nasara fara zama web designer.
Yauwa da kyau,yanzu kam! Ka gama da matsalar farko,abu na biyu da za ka a yanzu shine ya zan canza sunan shafin daga UNTITLE NOTAPAD zuwa mailittafi? Kar ka damu,a keyboard na ka sai ka latsa CTRL ,kar ka ɗaga yatsan ka,sai ka kuma danna S,watau ka ga ya zama CTRL da S kenan. Kuma kana dannawa zai baka wannan window na ƙasa.
Hoto 1.06,inda aka rubuta file name na nufin ka rubuta sunan shafin ka.
Idan ka ga wannan window ,sai ka je in da aka rubuta file name ka rubuta index.html, ka sani dole idan ka rubuta sunan,sai ka rubuta sunan yaren da yanar gizo ke amfani da shi na farko,domin idan babu wannan suna,shafin naka bai cika ba;kuma browser ba zata iya bu ɗe shi a yarda kake soba.Bayan ka rubuta sunan da kake so sai ka je a gida na biyu da aka rubuta TEXT DOCUMENTS;abinda ake nufi anan shin shin wane yare ya ke rubuce a shafin naka? Dubi hoto na 1.07
Hoto 1.07dubi hoton da kyau ba kuskure kuwa.
Index a nan babban abu ne mai mahimmamanci a shafin ka na farko,domin shine zai haɗa alaƙa da sauran shafukan da zaka iya buƙata a gaba,amma yanzu kam,mu dai je zuwa.To bayan ka gama rubuta Index.html a gidan farko da aka sa file name,sai ka je gida na gaba inda aka rubuta save as type,sai ka latsa ‘yar kibiyar da ta kalli ƙasa,zai baka rubutu,sai ka zaɓi all files,daga nan sai ka danna inda aka rubuta save.Ka na danna save zai bu ɗe maka allon rubutun ka,kuma idan ka duba a sama za ka ga cewa sunan ya canza daga untitle notepad zuwa index notepad
Hoto 1.08.Hey!!!!!yanzu kam!za a da kai,domin ka gama abu amai wuya.
Abinda kawai yanz ya rage shine bari in rubuta  wani abu a allon in gani in kai/ku za ku/ki/ka iya.
Hoto 1.09 ha ƙiƙa yanzu kam na rubuta wani abu a allon rubutu.
Idan ka a ka dubi allon rubutu na notepad a sama ,na yi rubutu,wanda rubutun yana cikin yaren gina yanar gizo watau tag,da kuma element.Idan an duba da kyau na rubuta <!doctype html> kamar yarda na bayyana da farko,dole ne a rubuta haka a duk kowane shafi in dai ya shafi na yanar gizo,amma sannu ahankali za a fahimci hakan,sai kuma na biyu daga  ƙasa inda na rubuta HTML,watau shafin yana ɗauke da ƙa’idojin gina yanar gizo.idan ka duba inda aka rubuta ,
Ku gafarce ni zan ci gaba daga Nura mailittafi.